-
Labanon : Ina Cikin 'Yancin Walwala A Saudiyya_Hariri
Nov 13, 2017 06:49A karon farko, tun bayan murabus dinsa na ba zata tun daga Saudiyya, firayi ministan Labanon, Saad Hariri, ya yi jawabi a gidan talabajin.
-
Shugaban Labanon Ya Tabbatar Da Cewa Sa'ad Hariri Na Tsare Ne A Saudiya
Nov 12, 2017 18:11Shugaban kasar Labanon Michel Aoun ya bayyana cewa firayi ministan kasar da ya sanar da murabus dinsa Sa'ad Hariri yana cikin wani irin yanayi mai daure kai sakamakon takurin zirga-zirga da yake fuskanta a kasar Saudiyya.
-
Labanon : Aoun, Ya Bukaci Bayani Daga Saudiyya Kan Batun Hariri
Nov 11, 2017 15:23Shugaban kasar Labanon, Michel Aoun, ya bukaci bayani daga gwamnatin Saudiyya akan abunda ke kawo cikas wajen komawar firayi ministan kasar mai murabus Saad Hariri komawa gida.
-
Abdul-Fatah Al-Sisi: Masar Ba Zata Shiga Wani Rikici Da Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Labanon Ba
Nov 08, 2017 06:13Shugaban kasar Masar ya bayyana cewar gwamnatinsa ba zata shiga cikin wani rikici da kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ba.
-
Wata Majiya: Hariri Yayi Murabus Ne Bayan Iran Ta Ki Yarda Da Bukatar Saudiyya Na Janye Goyon Bayan Al'ummar Yemen
Nov 05, 2017 18:13Wata majiya mai karfi ta bayyana cewar Sa'ad al-Hariri, firayi ministan kasar Labanon mai murabus, yayi murabus daga mukamin nasa ne bayan da Iran ta ki amincewa da bukatar da ya gabatar mata da sunan Saudiyya na ta daina goyon bayan al'ummar kasar Yemen da Saudiyyan take ci gaba da kai musu hare-hare.
-
Sayyid Nasrallah: An Tilasta Wa Hariri Murabus Ne, Ba Bisa Son Ransa Ba
Nov 05, 2017 18:12Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar an tilasta wa firayi ministan kasar, Sa'ad Hariri, yin murabus ne daga Saudiyya ba bisa son ransa ba, yana mai kiran al'ummar kasar da su kai zuciya nesa da kuma ci gaba da kokari wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.
-
Iran : Murabus Din Hariri, Makircin US-Saudi-Israila Da Nufin Kara Yanayin Zaman Dar-Dar A G/Tsakiya"
Nov 05, 2017 05:48Iran ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Bahram Qassemi, ta yi watsi da tuhumce-tuhumcen Sa'ad Hariri, tsohon firayi ministan Labanon mai murabus, tana mai cewa maganganun nasa sun yi daidai da tuhumce-tuhumce marasa tushe da Amurka da Sahyoniyawa da Saudiyya suke yi da nufin haifar da sabon rikici a kasar Labanon da kuma yankin Gabas ta tsakiya.
-
Sa'ad Hariri Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa Na Fira Ministan Kasar Lebanon
Nov 04, 2017 19:31Fira ministan kasar Lebanon Sa'ad Hariri ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa a lokacin da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar Saudiyya a yau Asabar bayan ya yi zargin cewa yana fuskantar barazanar kisan gilla.
-
Hizbullah: Gwagwarmaya Za Ta Iya Rusa Sabbin Manufofin Amurka A Gabas Ta Tsakiya
Oct 29, 2017 19:05Mataimakin shugaban Majalisar shawara ta Hizbullah Sheikh Ali Daa'mush ya ce; Amurka da Isra'ila da Saudiyya suna son kafa rundunar fada da Iran da kuma gwgawarmaya.
-
Wata Kotu A Kasar Lebanon Ta Bada Sammashin Kama Tsohon Priministan Kasar Libya Kan Sace Imam Sadr
Oct 13, 2017 19:03Wata kotu a kasar Lebanon ta bada sammashin kama tsohon Priministan kasar Libya Abdussalam Jalloud dangane da bacewar babban malamin addini kuma shugaban kungiyar Amal na kasar Immam Musa Sadr a shekara 1978 bayan wata ziyarar da aka gayyace shi a kasar.