Pars Today
Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya sanar da cewa, har yanzu ana aiwatar da ayyukan cin zarafin 'yan adama a wasu sassa na kasar Sudan ta kudu.
Ministan harkokin wajen kasar Sudan ya sanar da cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun amince da mika ragamar mataimakin shugaban kasa ga jagoransu Riek Machar a karkashin yarjejeniyar sulhu da aka cimma a kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Sudan ya bada sanarwan cewa yan tawayen Sudan ta kudu sun amince da cewa shugaban su Rick Macher ya koma kan kujerarsa ta mataimakin shugaban kasa a taron da suka gudanar a kasar Uganda a jiya Asabar.
Gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawaye sun cimma matsaya a game da ficewar Dakarun bangarorin biyu daga yankunan fararen hula a jiya juma'a
'Yan Majalisar kasar Sudan ta kudu sun fara tattaunawa kan yadda za a yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima ta yadda za a kara wa'adin shugaban kasa da na 'yan Majalisa zuwa shekara ta 2021.
Yan Majalisun Dokokin Kasar SUdan ta Kudu sun fara gudanar da muhawara kan karawa shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kiir wa'adin mulki zuwa shekara ta 2021.
Bangarorin da ke rikci da juna a kasar Sudan ta kudu sun zargi junasu da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimmawa 'yan kwanakin da suka gabata.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir da tsohon mataimakainsa jagoran 'yan tawaye na kasar, Riek Machar, sun amince da shirin tsagaita wuta na tsawan kwanaki uku.
Tattaunawa gaba da a za a yi tsakanin gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawayen kasar za ta fi mayar da hankali ne kan yadda 'yan gudun hijrar kasar za su koma gida daga kasar Uganda
A daren jiya ne aka fara gudanar da tattaunawar sulhu zagaye na biyu tsakanin gwamnatin kasar Sudan ta kudu da kuma bangaren 'yan tawayen kasar a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.