Pars Today
Limamin da ya jagoranci sallar idin lahiya a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ya bayyana cewa: Duk wani yaki da kasar Amurka zata kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yakin zai shafi babbar 'yar lelan Amurka a yankin.
A yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a kasar D/congo, ministan tattalin arzikin kasar ya bukaci 'yan adawa da su hau kan tebirin tattaunawa tare da gwamnati.
Gwamnatin Mali ta sanar da cewa ta koma kan kujerar tattaunawa da bangaren 'yan tawayen kasar bayan dakatar da zaman tun a shekara ta 2015 da ta gabata.
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kirayi gwamnatocin Sudan da kuma Sudan ta kudu kan su koma kan teburin tattaunawa dangane da batun sake shata iyakokin yankin Abey.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen Sudan Da Sudan Ta Kudu da su sake zama teburin tattaunawa a tsakaninsu don ayyana matsayin yankin Abyei da ke ci gaba da haifar da rikici a tsakaninsu.