Pars Today
Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da cewa ayyukan tabbatar da zaman lafiya da dakarunta suke yi a yammacin Afirka yana fuskanatar barazana saboda karancin kudade
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar tana fuskantar karancin kudade na daukan nauyin dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu a yankin yammacin Afrika.
Waziriyar kasar Jamus da a halin yanzu haka take gudanar da ziyarar aiki a kasar Senegal ta bukaci daukan matakan warware matsalolin bakin haure da 'yan gudun hijira.
Rundunar sojin kasar Burkina Faso ta sanar da cewa an samu nasarar kame sama da mutane 200 a wasu samame na hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaron kasashen Burkina Faso, Ghana, Benin da Togo da nufin fada da ta'addanci.
Shugabanin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO sun fara gudanar da taronsu karo na biyar da nufin lalubo hanya mai sauki na samar da kudin bai daya a tsakanin kasashen.