Pars Today
Shugaban kasar Zimbabwe ya jinjinawa kasar China kan irin goyon bayan da take bai wa Zimbabwe musamman a fuskar tattalin arziki da siyasa tare da bayyana aniyar kasarsa ta ci gaba da karfafa alaka da kasar ta China a bangarori da dama.
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar ci gaba da yaduwar rashin tsaro da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya wani lamari ne da zai cutar da dukkanin kasashen yankin.
A ranar Jumma'a 22 ga watan Disamban da muke ciki ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyarar ba zata zuwa jumhuriyar Niger, inda ya gana da sojojin kasar ta Faransa da ke can, ya kuma gana da shugaban kasar ta Niger.
Kakakin Kungiyar gwagwarmayar musulinci ta yankin Palastinu ya sanar da cewa yarjejjeniyar baya bayan nan da kungiyar da cimma da Gwamnatin Masar za ta aifar da gagarumin sauyi a yankin
Yan Majalisun Dokokin Tunusiya sun jaddada bukatar ganin gwamnatin kasar t hanzarta daukan matakin dawo da alakar jakadancinta da kasar Siriya.