Pars Today
Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya sake caccakar shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, dangane da ficewar da ya yi daga yarjejeniyar da aka cimmawa kan shirin Iran na nukiliya.
A karo na goma 12 Hukumar makamashin Nukiliya ta Duniya ta fitar da rahoto da yake tabbatar da cewa Iran tana aiki da yarjejeniyar
Babbar jami'a kan harkokin siyasar wajen kungiyar tarayya turai federica Mogherini ta jaddada cewa, za su ci gaba da yin aiki tukuru tare da kawayensu, domin ganin an kare yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran.
Jakadan kasar Iran a Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya ya ce: Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya "IAEA" a karo na goma sha biyu tana tabbatar da cewa: Iran tana ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da ita.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yau ya tuntubi shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ta wayar tarho, inda suka tattauna kan batutuwa daban-daban da suka shafi alaka tsakanin Faransa da Iran da kuma batun yarjejeniyar nukiliya.
Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran ya ce: Bakar siyasar kasar Amurka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata fuskanci maida martani mai gauni.
Jaridar The Wall Street Journal ta kasar Amurka ta fallasa makircin gwamnatin Amurka da na Haramtaciyar kasar Isra'ila kan zargin da suka yi cewa: Kasar Iran tana shirya kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasashen Turai.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya, sun jaddada wajabcin ci gaba da yin aiki da ita kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.
Kakakin babbar jami'a mai kula da siyasar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai ta jaddada cewa: Kungiyar tarayyar Turai zata ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da duniya ta cimma da kasar Iran.
Ministan kudi na kasar FaransaBruno Le Maire ya ce; Har yanzu Faransa ba ta karbi jawabi daga Amurka ba dangane da bukatar da ta aike tare sauran kasashen turai na neman kada a sa wa kamfanoninsu masu aiki a Iran takunkumi