-
Kotun ICC Ta Daure Tsohon Shugaban Sabiyawa, Karadzic Shekaru 40
Mar 25, 2016 00:23Kotun duniya mai shari'ar manyan laifukan yaki ta yanke wa tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic hukunci daurin shekaru 40 a gidan yari saboda samunsa da hannu dumu dumu cikin kisan kiyashi da aka yi wa wasu musulmai yanki Srebrenica a shekarar 1995.