-
Amurka Ta Aike Da Wasu Fursunonin Guantanamo Zuwa Kasar Senegal
Apr 04, 2016 17:42Ma'aikatar tsaron kasar Amurka, Pentagon, ta sanar da tusa keyar wasu 'yan kasar Libiya su biyu da sojojin Amurkan suke tsare da su a gidan yarin nan na Guantanamo da ke kasar Cuba na tsawon shekaru zuwa kasar Senegal don ci gaba da tsare su a can.