Pars Today
Koriya ta Arewa ta danganta sabon takunkumin da Amurka ta kakaba mata a matsayin shelanta yaki kan ta.
A wani lokaci nan gaba ne aka sa ran, shugaba Donald Trump na AMurka, zai sanar da takunkumin kasarsa mafi girma da ba'a taba kakaba irinsa ba kan Koriya ta Arewa.
Mahukuntan Pyongyang, sun soke wata ganawa da aka shirya wasu manyan jami'an kasar zasu yi da sakataren gwamnatin Amurka, Mike Pence, a daura da gasar Olympics ta hunturu a birnin Pyeongchang, na Koriya ta Kudu.
Kasar Amurka ta sanya matsin lamba kan kasashen nahiyar Afrika domin su yanke alakar jakadanci da kasar Koriya ta Arewa.
Wata cibiyar bincike mai rajin kawo sulhu da zaman lafiya a duniya dake birnin Stolkhom na kasar Sweden ce ta bayyana hakan.
Gwamnatin Koriya ta Arewa ta sanar da cewa kasar za ta ci gaba da karfafa shirinta na nukiliya duk kuwa da matsin lambar da kasar ta ke fuskanta a wannan bangaren.
Bayan watsa labarin cinikayyar Man fetir tsakanin buranan Beijing da Pyongyang, Shugaban Amurka Donal Trump ya zargi hukumomin China da karya takunkumin da MDD ta kakabawa Korea ta Arewa ta hanyar sayar mata da man fetir.
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sake sanya wa kasar Koriya ta Arewa wani sabon takunkumi sakamakon sake gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango da kasar ta yi.
Shugaba Kim Jung Un, ya ce makaman Nukiliyar da muke da su sun maida mu zama babbar barazanar da Amurkan take fuskanta.
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da bayani da a ciki ya bayyana wajabcin bude kafar tataunawa da Korea ta Arewa domin rage zaman dar-dar a yankin.