Pars Today
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Int. ta yi kakkausar suka dangane da hukuncin kisa da kotun kasar Masar ta yanke a kan wasu 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi (Muslim Brotherhood).
Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama ta Amnesty International ta yi tofin Allah tsine kan yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin 75 da kotun da ke shari'ar manyan laifuka A Masar ta zartar a yau Asabar.
Kungiyar ta Amnesty ta zargi kwamandojin sojojin kasar ta Myanmar da tafka laifukan yaki akan al'ummar musulmin Rohingya
Gwamnatin kasar Kamaru ta musanta rahoton da kungiyar kare hakkokin bil'adaman na ta Amnesty International ta fitar kan rikicin da ke faruwa a yankin masu magana da harshen Ingilishi na kasar tana mai bayyana rahoton a matsayin tsagoron karya kawai.
Rundunar sojin Nijeriya ta mayar da martani ga rahoton kungiyar kare hakkokin bil'adama din nan ta kasa da kasa Amnesty International da ya zargin sojojin da yin fyade da sauran nau'oi na cin zarafin mata a sansanonin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno.
Kungiyar kare hakkin bil'adaman ta kasa da kasa daga ofishinta da ke birnin London ta bukaci da a gudanar da bincike mai cin gashin kanshi dangane da amfani da karfi akan al'ummar Palasdinu da 'yan sahayoniya su ke yi.
Kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar Masar ke ci gaba da take hakkin 'yan adawa a kasar
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta zargi gwamnatocin kasashen turai da hannu a cin zarafin da ake yi wa bakin haure da 'yan gudun hijira a Libiya.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta yi tir da matakin hukumomin Aljeriya na korar 'yan Afrika zuwa gida.
Kungiyar Amnesty International ta zargi shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, da kokarin rufa-rufa kan kisan kiyashin da akayiwa musulmin Rohingyas a Jihar Rakhine, wanda MDD ta bayyana a matsayin na kare dangi.