Pars Today
Jaridar Asshuruq ta kasar Masar ta bada labarin cewa: Bullar matsalar karancin kudi a kungiyar hadin kan kasashen Larabawa tana ci gaba da janyo koma baya a harkar tafiyar kungiyar tare da yin murabus din wasu daga cikin jami'anta.
Kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa da haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a cikin yankunan Palastinawa, musamman a gabashin birnin Quds.
An Soli Halin Ko In Kula na kasashen larabawa akan kasar libya
Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta jaddada goyon bayanta ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta tare da jaddada hakkin Palasdinawa na gwagwarmaya domin kwato hakkokinsu.
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya yi kakkausar suka kan yadda duniya ta kau da kai daga kan irin mummunan halin da al'ummar Palasdinu suka shiga ciki.
Kasar Maroko da wasu gungun kasashen Larabawa sun haramta zaman taron hadin gwiwa da aka shirya gudanarwa tsakanin kasashen Afrika da na Larabawa a kasar Equatorial Guinea
Jakadan Iran kana kuma wakilin kasar na dindindin a Majalisar Dinkin Dinkin Gholam Ali Khoshroo ya yi watsi da zargi 'maras tushe' da wasu kasashen larabawa suka yi na cewa Iran tana tsoma musu baki cikin harkokinsu na cikin gida.
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya yi suka kan rashin samun daidaiton baki a tsakanin manyan kasashen duniya dangane da hanyar warware rikicin kasar Siriya.
"Yan Sahayoniya Na Yawaita Yi wa Masallacin Kudus Kutse
Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta bayyana shirin kera makaman nukiliya da na kare dangi na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyan yankin gabas ta tsakiya.