Pars Today
Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kan wajen binciken ababan hawa a garin Zliten da ke gabashin birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka kashe sojojin gwamnatin kasar hudu.
Majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da hallakar 'yan ta'adda ISIS 13 a yayin gumurzu da Sojoji a gabashin kasar
Majiyar jami'an tsaro na kasar Libya ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe yan ta'adda na kungiyar Daesh 13 a fafatawa da su a gabacin kasar
Gwamnatin Somaliya ta sanar da hallaka mayakan Al-Shabab 87 yayin arangama da jami'an tsaro a kudancin kasar.
Kimanin mutum 18 ne suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan boko haram suka kai yankin tabkin Tchadi.
Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Niger ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar halaka mayakan kungiyar Boko Haram akalla 10 a yankin kudu maso gabashin kasar.
Kungiyar ta'ddanci ta Al-Shabab ta Somaliya ta mamaye wani yanki mai muhimmanci a Puntland mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar ta Somaliya.
Wata majiyar sojin Nigeriya ta sanar da cewa: Sojojin kasar 23 ne suka bace babu labarinsu bayan da suka fuskanci harin mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram a garin Bama da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin kasar.
Sojojin kasar Somaliya sun ba da labarin cewa a wani gumurzu da suka yi da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab a kudancin kasar, sun sami nasarar hallaka 7 daga cikin 'yan ta'addan.
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: Tun daga farkon watan Janairun wannan shekara zuw yanzu 'yan ta'adda da yawansu ya kai 60 ne suka mika kansu ga jami'an tsaron kasar.