Pars Today
Wata majiyar tsaron kasar kamaru ta sanar da cewa mayakan kungiyar boko haram sun kai wani harin ta'addanci a wani kauye dake arewacin kasar
'Yan sandan kasar ta Somaliya sun ce mutane sun mutu ne saboda tarwatsewar wata mota da aka makare da bama-bamai a babban birnin kasar Magadishu.
Gargadin ya fito ne daga jami'an gwamnati da sojoji da suka yi taro da 'yan kasuwar yankin Difa a yankin kudu maso gabacin kasar.
Babban mai gabatar da kara na kasar Libya ya bada sanarwan samun umurnin kama mutane kimani 830 wadanda ake tuhuma da kasancewa cikin kungiyar yan ta'adda ta ISIS a duk fadin kasar.
Jiragen yakin gwamnatin kasar Rasha a Syria sun yi ruwan boma bomai a kan babbar cibiyar yan ta'adda a birnin Idlib na kasar ta Siria.
Kasar Siriya ta bayyana cewar Amurka, Birtaniyya da kawayensu suna goyon bayan 'yan ta'addan da suke yaki a kasar ta hanyar taimaka musu da sinadarori masu guba bugu da kari kan nau'oi daban-daban na makamai.
Ma'aikatar cikin gidan kasar Masar ta sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kashe wasu 'yan ta'adda su uku da ake zargin suna da hannu cikin harin da aka kai wa kiristoci kibdawa na kasar a kwanakin baya.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Faransa ya sanar da cewa: 'Yan kasar Faransa 271 ne suka koma gida bayan gudanar da yaki karkashin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Iraki da Siriya.
Dakarun kungiyar Hizbullah da sojojin Siriya sun sami nasarar kwato wasu yankuna da kauyuka alal akalla guda 9 da suke kan iyakokin kasashen Siriya da Labanon daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Jabhatun Nusra a hare-haren da suka kaddamar a jiya Juma'a.
Dubban masu rajin kare hakkin bil'adama yan kasar Algeria sun maida martani kan furucin jakadan kasar Saudia a birnin Algies kan kungiyar Hamas ta al-ummar Palasdinu.