-
Kwamitin Tsaron MDD Zai Tattauna Batun Harin Turkiyya Kan Kurdawan Siriya A Yau
Feb 16, 2016 05:48A wani lokaci a yau din nan Talata ne membobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai su gudanar da wani zama na sirri don tattauna batun hare-haren soji da kasar Turkiyya take kai wa Kurdawan kasar Siriya a cikin kasar ta Siriya.