Pars Today
Kungiyar tarayyar Turai ta yi Allah wadai da hukuncin kisa da wata kotu a Masar ta yanke kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi.
Gwamnatin Masar ta bakin ma'aikatar harkokin wajenta ta bayyana baynin da ya fito daga Majalisar Dinkin Duniyar da cewa ba abin da za a lamunta da shi ba ne.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Int. ta yi kakkausar suka dangane da hukuncin kisa da kotun kasar Masar ta yanke a kan wasu 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi (Muslim Brotherhood).
Kotun da ke shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira na kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin su 75 tare da zartar da hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku kan wasu 46 na daban.
Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama ta Amnesty International ta yi tofin Allah tsine kan yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin 75 da kotun da ke shari'ar manyan laifuka A Masar ta zartar a yau Asabar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato cewa bom din ya fashe ne akan titin Simon Bolivar da ke birnin al-kahira, inda nan ne ofishin jakadancin Amurka yake.
Kasashen Masar da Sudan sun cimma wata muhimmiyar yarjejeniya kan sabanin da ke tsakaninsu dangane da ruwan tekun maliya da ya ratsa kasashensu.
Majiyar jami'an tsaro a kasar Masar ta bayyaba cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata sun halaka yan ta'adda a kalla 20 a yankin Sinaa.
Kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahira ta yanke hukuncin kisa wasu mutum 6 a jiya Talata.
Wata kotu a kasar Masar ta cire sunayen mutane kimani 1500 daga jerin sunayen yan ta'adda a kasar daga ciki har da sunan tsohon shugaban kasar Mohammad Mursi.