• Akalla Mutane 50 Sun Mutu Sakamakon Harin Boko Haram A Jihar Borno

    Akalla Mutane 50 Sun Mutu Sakamakon Harin Boko Haram A Jihar Borno

    Jan 31, 2016 12:16

    Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar alal akalla mutane 50 sun rasa rayukansu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon wani hari da wasu mahara da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai kauyen Dalori da ke kusa da birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.