Pars Today
Rundunar sojin kasar Rasha ta aike da wasu manyan makaman kariya zuwa sansanin sojin Rasha da ke Yankin Hamimim a cikin gudumar Latakia a arewacin Syria.
Kasar Rasha ta sanar cewa nan ba da jimawa ba za ta mikawa gwamnatin Siriya makaman garkuwa na S-300.
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta gabatar da cikakken rahoto dangane da yadda aka harbo jirgin yakin kasar a lardin Lazikiyya na kasar Siriya tana mai dora alhakin faruwar hakan a wuyanharamtacciyar kasar Isra'ila.
Ma'aikatar harkokin wajen China, ta kirayi jakadan AMurka a birnin Pekin, domin bayyana masa fishin kasar akan takunkumin da Amurkar ta kakaba wa wani bengaren sojin kasar, saboda sayen makaman yakin Rasha.
Gwamnatocin Rasha da China sun gargadi gwamnatin Trump dangane da takunkumin da ta dora wa rundunar sojin China, saboda sayen makamai daga Rasha.
A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta fitar a dazu, ta ce jiragen yakin Isra'ila sun yi garguwa da jirgin Saman Rasha da aka harbo
Wani jirgin sojin Rasha ya bace a daren jiya, a daidai lokacin da Isra'ila take kaddamar da wasu hare-hare a birnin Latakia da ke gabar ruwa a arewa maso yammacin kasar Syria.
Majiyar sojoji kasar Rasha a kasar Siriya ta bayyana cewa jirgin saman yakin kasar ya bace a yankin lantakiya na kasar tare da sojoji 14 a cikinsa a jiya da yamma.
Ma'akatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa a yau rundunar sojin kasar ta fara gudanar da wani atisayi mafi girma a yankin gabashin kasar.
Hukumar zabe a kasar Rasha ta bayyana sakamakon zaben gama gari wanda aka gudanar a jiya lahadi a yau litinin.