-
Ayat. Kermani: Saudiyya Ta Fada Tarkon Amurka Da Yahudawan Sahyoniya
Jun 10, 2016 18:13Na'ibin limamin Juma'ar birnin Tehran Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani yayi kakkausar suka ga siyasar nuna kiyayyar ga al'ummomin yankin Gabas ta tsakiya da Saudiyya ta ke gudanarwa yana mai cewa Saudiyyan ta fada tarkon Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Ayat. Emami Kashani: Makiya Na Neman Bangaren Raunin Al'ummar Iran Ne Don Cutar Da Su
Apr 08, 2016 15:25Ayatullah Muhammad Emami Kashani, daya daga cikin mataimakan limamin Juma'ar birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ja kunnen al'ummar kasar da su yi taka tsantsan dangane da ci gaba da kokarin makiyansu na ganin sun cutar da su a duk lokacin da suka sami wata dama.
-
Ayat. Muwahhidi Kermani: Saudiyya Na Ba Da Cin Hanci Don Sanya Hizbullah Cikin 'Yan Ta'adda
Mar 18, 2016 16:18Na'ibin limamin juma'ar birnin Tehran Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani ya bayyana cewar kasar Saudiyya tana ba wa kasashen larabawa cin hancin don dai su goyi bayanta wajen siffanta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a matsayin kungiyar ta'addanci, yana mai kakkausar sukar kasar Amurka sakamakon irin goyon bayan da take ba wa Saudiyya duk kuwa da ci gaba da kashe al'ummar kasar Yemen da take yi.
-
Limamin Juma'ar Tehran Yayi Allah Wadai Da Sanya Hizbullah Cikin Kungiyoyin Ta'addanci Da Larabawa Suka Yi
Mar 04, 2016 15:55Na'aibin limamin Juma'ar birnin Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami yayi Allah wadai da sanya kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon cikin kungiyoyin ta'addanci da kungiyar kasashen larabawan Tekun Fasha ta yi, yana mai bayyana hakan a matsayin hadin baki da haramtacciyar kasar Isra'ila.