Pars Today
A safiyar yau Lahadi ce aka fara zaben majalisun larduna a kasar Siriya wanda yake nuna cewa an koma ga tsarin democradiya da gaske a kasar.
A daren jiya Asabar ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta harba makamai masu linzami a kan filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria, amma makaman kariya na rundunar sojin Syria sun kakkabo su.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa yakar yan ta'adda wadanda suke iko da birnin Idlib na kasar Siriya wajibi ne.
Manzon Musaman na MDD kan Kasar Siriya ya fara tattaunawa da wakilan kasashen Rasha da Iran gami da Turkiya a Hedkwatar Majalisar dake birnin Ganeva.
Majiyar gwamnatin Siriya ta sanar da cewa: Daya daga cikin jagororin kungiyar ta'addanci ta Jubhatun-Nusrah da suke da hannu a harhada makamai masu guba a kasar Siriya ya nemi mafaka a kasar Turkiyya.
An kammala zaman taron shugabannin kasashen Rasha, Iran da kuma Turkiya, wanda aka gudanar yau Juma'a a birnin Tehran na kasar Iran a kan batun rikcin kasar Syria, da kuma ci gaba da nemo hanyoyin warware rikicin.
Shugaban kasar Rasha Viladimin Putin ya iso birnin tehran domin halartar taro kan birnin Idlib na kasar Siriya
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bakin kakakinta Maria Zakharova ce ta bayyana cewa kasar tana ba da cikakken goyon baya ga gwamnatin Syria a yakin da take yi da 'yan ta'adda
Wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Iran Sadiq Husain Jabiri Ansari ya ce; Tuni an kammala tsara bayanin bayan taron na bangarori uku a Tehran
Ma'aikatar harkokin wajen Syria ta fitar da bayani da a ciki ta bayyana cewa; Amurka da kawayenta suna ba da makamai ga 'yan ta'addar kungiyar Nusrah da kuma Da'esh