-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Mutuwar Sojoji 5 A Harin Boko Haram
Oct 31, 2016 05:25Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa wasu sojojin kasar su 5 sun rasa rayukansu kana wasu 19 kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kwanton bauna da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram suka kai musu a kudancin jihar Borno.
-
An Fara Gudanar Da Bukukuwan Tunawa Da Kallafaffen Yaki A Iran
Sep 21, 2016 12:04Bangarori daban-daban na sojojin Iran sun gudanar da gagarumin fareti da gwajin nau'oi daban-daban na makamai a ranar farko na bukukuwan Makon Kariyar don tunawa da zagayowar shekaru 36 da zagayowar kallafaffen yaki na shekaru takwas da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafawa Iran.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Ce: Babu Kabilanci Cikin Korar Wasu Manyan Sojojin Kasar
Jun 14, 2016 05:32Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotanin da wasu kafafen watsa labarai suke yadawa na cewa akwai wariya cikin ritayar da aka yi wa wasu manyan jami'an sojin kasar da nufin fifita arewacin kasar a kan kudanci.
-
Rundunar Sojin Nigeria Ta Musanta Zargin Kisan 'Yan Biafra Da Amnesty Ta Yi Mata
Jun 10, 2016 18:14Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkokin bil'adama ta kasa da kasa, Amnesty International inda ta zargi sojojin da kashe wasu wasu mutane marasa makami masu goyon bayan kafa Jamhuriyar Biafra alal akalla 17.
-
'Yan Kungiyar PKK Sun Hallaka Wasu Sojojin Kasar Turkiyya 4
May 01, 2016 16:51Rahotanni daga kasar Turkiyya sun bayyana cewar alal kalla sojojin kasar Turkiyya guda hudu sun mutu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon wasu hare-hare da 'yan kungiyar PKK ta Kurdawa da gwamnatin ta haramta suka kai wa dakarun gwamnatin a yankunan Gaziantep da Mardin da ke kudu maso gabashin kasar ta Turkiyya.
-
Janar Pourdestan: Sojojin Iran Za Su Ci Gaba Da Ayyukan Da Aka Tura Su Yi A Siriya
Apr 18, 2016 05:21Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Iran Birgediya Janar Ahmad Ridha Pourdestan ya bayyana cewar sojojin Iran da suke kasar Siriya a matsayin masu ba wa sojojin kasar shawara za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a can a ci gaba da taimakon da suke ba wa sojojin a fadar da suke yi da 'yan ta'adda.
-
Iran Ta Sanar Da Tura Wasu Sojojinta Na Musamman Zuwa Siriya
Apr 04, 2016 17:30Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tura wasu dakarun sojojinta na kasa na musamman zuwa kasar Siriya a ci gaba da taimakon da Iran take ba wa sojojin Siriya a fadar da suke yi da kungiyoyin ta'addancin da aka shigo da su kasar daga kasashen duniya daban-daban.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Ceto Mutane 63 Daga Hannun Boko Haram
Mar 04, 2016 16:12Rundanar sojin Nijeriya ta sanar da samun nasarar kwato wasu mutane 63 daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka garkuwa da su bayan da sojojin suka fatattaki ‘yan ta’addan daga wasu kauyuka da yankuna na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriyan.
-
Iran Ta Sanar Da Wasu Matakai Na Kare Kanta Daga Wuce Gona Da Irin Makiya
Feb 12, 2016 04:58Mataimakin kwamandan sojojin sama na Iran Birgdeiya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewar sojojin saman na Iran suna shirin fara sanya wa jiragen saman yakin kasar samfurin F-14 Tomcat sabon makami mai lizamin nan samfurin Nasr da suka karba a kwanakin baya daga wajen ma'aikatar tsaron kasar.