-
Kenya: Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutane 7
Jun 18, 2018 07:42Kakakin 'yan sandan kasar Kenya Charles Oyino ne ya sanar da cewa an dasa bom din ne a bakin hanya a gabacin kasar wanda kuma ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai
-
Moroko: An kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da 180 A Cikin Shekara Guda
Jun 18, 2018 07:39Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ne ya nakalto majiyar tsaron Moroko na cewa an kashe 'yan ta'addar ne acikin shekarar 2017 da ta gabata.
-
Mutane Akalla 16 Suka Rasa Rayukansu Sanadiyar Guguwa Da Ruwan Sama A Jihar Bauchi
Jun 18, 2018 03:42Mutane akalla 16 aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar isga da mamakon ruwan sama a jihar Bauci arewa maso gabacin tarayyar Najeriya a ranar Asabar da ta gabata.
-
Habasha Da Somalia Sun Bukaci A Yaki Ta'addanci
Jun 17, 2018 13:05Shugabannin kasashen Somaliya da Habasha sun bukaci hadin gwiwar kasa da kasa domin yakar ayyukan ta'addanci a doron duniya.
-
Najeriya : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 31 A Borno
Jun 17, 2018 11:46Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake biyu da ake danganta wa dana kungiyar Boko Haram a shiyar arewa maso gabashin kasar.
-
Kamaru: An kashe Mutane 3 A Harin Ta'addanci
Jun 17, 2018 07:38Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar sin ya ambato majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa mutane 3 sun mutu ne sanadiyyar harin kunar bakin wake da aka kai a yankin Limani da ke arewacin kasar ta kamaru
-
Majalisar Kasar Kongo Na Shirin Kafa Dokar Ba Da Kariya Ga Tsoffin Shugabannin Kasar
Jun 17, 2018 01:21Majalisar kasar Demokradiyyar Kongo ta sanar da cewa nan gaba kadan za ta gudanar da wani zama na musamman don tattauna bukatar da shugaban kasar Josepj Kabila ya gabatar mata na kafa wata doka da za ta ba wa tsoffin shugabannin kasar wata kariya ta musamman.
-
Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Tsakanin Kasashen Saudiyya Da Moroko
Jun 17, 2018 01:20Kakakin gwamnatin kasar Moroko yayi kakkausar suka ga matsayar da kasar Saudiyya ta dauka na kin kada kuri'ar goyon bayan kasar Morokon a kokarinta na daukar bakuncin gasar kwallon kafa na duniya a shekara ta 2026.
-
Kamaru Ta Musanta Zargin Amnesty International Kan Rikicin Yankin Masu Magana Da Ingilishi
Jun 17, 2018 01:19Gwamnatin kasar Kamaru ta musanta rahoton da kungiyar kare hakkokin bil'adaman na ta Amnesty International ta fitar kan rikicin da ke faruwa a yankin masu magana da harshen Ingilishi na kasar tana mai bayyana rahoton a matsayin tsagoron karya kawai.
-
Jami'an Tsaron Nijar Sun Kame Ton Uku Na Tabar Wiwi A Kasar
Jun 17, 2018 01:16Rahotanni daga kasar Nijar sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame ton uku na tabar wiwi da aka shigo da ita kasar, a wani abu da ake ganinsa a matsayin mafi girman nasarar da jami'an tsaron suka samu a wannan fagen.