-
Zimbabwe : An Haramta Zanga-zanga Kan Karin Haraji
Oct 10, 2018 02:14Rundunar 'yan sanda a Zimbabwe, ta haramtawa kungiyoyin kwadago na kasar gudanar da zanga-zangar nuna adawa da karin haraji kan aikewa da kudade.
-
Ministan Kudin Afrika Ta Kudu Ya Yi Murabus
Oct 10, 2018 02:12Ministan kudin Afrika ta Kudu, Nhlanhla Nene, ya yi murabus daga mukaminsa, bayan kwashe kwanaki na kiraye kirayen hakan daga 'yan adawa bisa zarge zargen rashawa.
-
Kasashen Masar Da Tunusiya Da Aljeriya Za Su Yi Zama Kan Kasar Libiya
Oct 09, 2018 15:35Ministan harakokin wajen kasar Aljeriya ya ce nan ba da jimawa ba kasashen Masar da Tunusiya gami da kasarsa za su gudanar da zama kan rikicin kasar Libiya a birnin Alkahira.
-
Gwamnatin Masar Zata Hukunta Mutanen Da Suka Ki Gudanar Da Zabuka A Kasar
Oct 09, 2018 08:31Kwamitin kula da zabuka a kasar Masar ya sanar da cewa: Suna ci gaba da tantance sunayen mutanen da suka ki kada kuri'a a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Masar da nufin mika su ga ma'aikatar shari'ar kasar.
-
Da'awar Lashe Zabe Da Wani Dan Adawa Ya Yi A Kamaru Ya Fuskancin Allah Wadai
Oct 09, 2018 08:30Jam'iyya mai mulki a Kamaru da gwamnatin kasar sun yi suka kan matakin da daya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar ya dauka na shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.
-
An Gano Wani Babban Kabari Mai Dauke Da Tarin Gawawwakin Mutane A Garin Sirt Na Libiya
Oct 09, 2018 08:20Wata majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da gano wani babban kabari mai dauke da tarin gawawwakin mutane a yankin yammacin garin Sirt na kasar.
-
Wani Yariman Kasar Saudiyya Ya Kira Yi Al'ummar Kasar Da Su Yi Tawaye
Oct 09, 2018 03:45Yarima Khalid Bin Farhan ali Sa'ud ya bayyana cewa matukar ta tabbata cewa an kashe dan jaridar kasar Jamal Khashoogi to ya zama wajibi da a samar da sauyi a fagen siyasar kasar
-
Maroko: 'Yan ci-Rani Fiye Da 600 Sun Tsira Daga Halaka
Oct 09, 2018 03:18Sojan ruwan kasar Maroko ne su ka sanar da tseratar da 'yan ci-rani 615 daga nustewa a cikin ruwa a ckin tekun Mediterranea
-
Lavrov Ya Yi Soka Akan Yadda Kasashen Turai suke Tsoma Bakinsu A Harkokin Kasar Libya
Oct 09, 2018 03:17Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov da ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwuiwa da takwaransa na Italiya,Enzo Moavero Milanesi, a jiya Litinin a birnin Moscow ya ce tsoma bakin na kasashen trurai yana kara zuzuta wutar rikici
-
Masar: An Kama Dan Ta'adda Mafi Hatsari A Kasar Libya
Oct 09, 2018 03:14Kakakin sojojin kasar Libya masu biyayya ga Halifa Haftar ya sanar da cewa sun kama dan ta'addar kasar Masar mafi hatsari a garin Derna a jiya Litinin.