Ministan Kudin Afrika Ta Kudu Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33547-ministan_kudin_afrika_ta_kudu_ya_yi_murabus
Ministan kudin Afrika ta Kudu, Nhlanhla Nene, ya yi murabus daga mukaminsa, bayan kwashe kwanaki na kiraye kirayen hakan daga 'yan adawa bisa zarge zargen rashawa.
(last modified 2018-10-10T02:12:50+00:00 )
Oct 10, 2018 02:12 UTC
  • Ministan Kudin Afrika Ta Kudu Ya Yi Murabus

Ministan kudin Afrika ta Kudu, Nhlanhla Nene, ya yi murabus daga mukaminsa, bayan kwashe kwanaki na kiraye kirayen hakan daga 'yan adawa bisa zarge zargen rashawa.

A jiya Talata ne Mista Nene, ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasar Cyril Ramaphosa, wanda kuma ya amince da hakan.

Tuni dai shugaba Ramaphosa ya nada Tito Mboweni a matsayin sabon ministan kudin kasar bayan murabus din tsohon ministan kudin kasar.

Sabon ministan dai ya taba rike mukamin gwamnan babban bankin kasar, kuma gabanin hakan, shi ne ministan kwadagon Afrika ta kudun.

Ramaphosa ya ce, wanda ya gabaci Mboweni a wannan mukami wato tsohon ministan Nene, ya mika takardar yin murabus daga mukaminsa ne a jiya Talata, inda ya nemi sauka daga mukamin ministan kudin kasar bayan da aka zarge shi da yin alaka da iyalan attajirin nan Gupta wandanda keda alaka da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma wadanda ake zargi da hannu a wata badakalar karkata kudaden al'umma.