Sharhi : Halin Da Ake Ciki A Mali, Bayan Kisan Fulani 135
A Mali, kwana guda bayan kisan gillan da aka wa fulani makiyaya su 135 a kauyen Ogossagou, dake jihar Mopti, gwamnatin kasar ta rusa kungiyar 'yan kabilar Dogon masu dauke da makamai, da ake zargi da aikata kisan gillar.
Haka kuma gwamnatin kasar ta kori wasu manyan sojojin kasar ciki harda babban hafsan sojin kasar, bayan harin wanda shi ne irinsa mafo muni da aka taba gani a kasar a cikin shekaru shida.
Gwamnatin ta dau matakin ne a yayin wani taron majalisar ministocin kasar na gaggawa da shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita ya kira a jiya Lahadi.
Bayan taron ne fira ministan kasar, ya ce an rusa kungiyar ta ''Dan Nan Ambassagou'' wacce a hukumance take da'awar kare 'yan kabilar Dogon a tsakiyar kasar.
Taron ya kuma dauki matakin korar babban hafsan sojin kasar, da kuma na rundinar sojin kasa, da kuma na rundinar sojin sama, kamar yadda firaministan kasar Soumeylou Boubeye Maïga ya sanar wa manema labarai.
Harin a cewar hukumomin kasar ya yi sanadin mutuwar fararen hula galibi fulani su 135, da suka hada da mata da kuma yara, sai kuma wasu kimanin 50 da suka raunana.
Wata tawagar gwamnatin kasra data kunshi, ministoci, ta isa yankin da lamarin ya faru domin ganawa da iyalen wadanda lamarin ya rusa dasu da kuma mutane 43 da suka raunana a harin.
Hukumomin kasar sun sha alwashin daukar matakai na kare jama'ar kauyen tan hanyar tabbatar da tsaro, inda tuni aka jibge sojoji a yankin.
Da yake karin haske kakakin gwamnatin kasar, Amadou Koïta,, ya ce abunda suka gani, hankali baya iya daukansa, sun gane wa idannunsu yara da mata wadanda aka kona kurmus.
Gwamnatin ta kuma sha alwashin kame duk wadanda suke da hannu a wannan aika-aikar da kuma tabbatar da shari'a, inda a cewar mai shigar da kara na gwamantin jihar Mopti, tuni aka kaddamar da bincike.
Lamarin dai ya fusata 'yan kasar ta Mali, inda 'yan adawar kasar ke ganin matakin da gwamnatin kasar ta dauka bayan lamarin bai isa ba, inda suke bukata da a kori harda ministoci dake kula da sha'anin tsaron al'umma.
Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da wata tawagar kwamitin tsaro na MDD, ke ziyara a kasar ta Malin da kuma makobciyarta Burkina faso.
Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres, ya ce ya kadu matuka da kisan da akayi wa wasu fulani a tsakiyar kasar Mali.
Mista Guteres, ya bukaci hukumomin kasar Mali dasu gudanar da bincike cikin gaggawa kan wannan aika-aikar, domin gurfadar da duk wadanda suke da hannu a lamarin gaban shari'a.