Mar 26, 2019 02:59 UTC
  • Mali : Adadin Fulanin Da Aka Kashe Ya Kai 160

A Mali, adadin fulanin da aka kashe a kauyen Ogossagou dake jihar Mopti a tsakiyar kasar ya kai 160, a yayin da kuma wasu majiyoyi ke cewa adadin zai iya wuce ma hakan.

Harin wanda ake dangantawa dana mafarauta 'yan kabilar Dogon, shi ne irinsa mafi muni da aka taba gani a wannan kasar ta mali a cikin watanni shida

Shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita, wanda ya ziyarci kauyen da lamarin ya faru, ya baiwa sabon babban hafsan sojin kasar Janar Abdulay Kulibali, umarnin tabbatar da tsaro a yankin.

A ranar Lahadid ata gabata ne, shugaba Keita, ya kori manyan hafsoshin sojin kasar bayan bayan kazamin harin da aka kaiwa fulanin, da kuma rusa kungiyar mayakan 'yan kabilar ta Dogon da ake zargi da aika aikar.

Shugaban kasar wanda kuma ya ziyarci makeken kabarin da aka binne mutanen da aka kashe, ya sha alwashin ganin an gudanar da shari'a domin hukunta wadanda suke da hannu a kisan.

Tags