-
IAEA: Iran Tana Aiki Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Kan Shirinta Na Makamashin Nukiya
Feb 25, 2017 03:13Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta fitar da rahoton cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki da dukkanin yarjejeniyar da aka cimma kan shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya.
-
Jagoran Juyi: Fada Da Zalunci Da Munafinci Shi ne Biyayya Ga Imamai Ma'sumai ( a.s)
Feb 24, 2017 15:39Ayatullah Sayyid Ali Khamnei da ya ke jawabi a yayin tunawa da shahadar Fatima Zahra (a.s) ya ce: Manzon Allah da Iyalansa tsarkaka sun yi gwagwarmaya da zalunci.
-
Kawo Karshen Zaman Taron Kasa Da Kasa Kan Nuna Goyon Baya Ga Gwagwarmayar Al'ummar Palasdinu
Feb 23, 2017 01:43A yammacin jiya Laraba ne shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ya jagoranci rufe zaman taron kasa da kasa kan nuna goyon baya ga gwagwarmayar al'ummar Palasdinu da ake zalunta karo na shida a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Ruhani: Matsalar Palastinu Wata Alama Ce Ta Gazawar Kungiyoyin Kasa Da Kasa
Feb 22, 2017 14:29Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar matsalar Palastinu ba matsala ce ta wata al'umma guda ba, face wata alama ce ta zalunci da take hakkoki wasu al'ummomi kana wani lamari da ke nuni da gazawar cibiyoyin kasa da kasa.
-
Mahalarta Taron Goyon Bayan Intifada Sun Bukaci Kasashen Musulmi Su Rufe Ofisoshin Jakadancinsu A Amurka
Feb 22, 2017 14:28Mahalarta taron kasa da kasa kan goyon bayan Intifadar al'ummar Palastinu da aka gudanar a nan birnin Tehran sun bukaci gwamnatocin kasashen musulmi da su rufe ofisoshin jakadancinsu da ke Amurka matukar dai gwamnatin kasar ta mayar da ofishi jakadancinta dake haramtacciyar kasar Isra'ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Qudus.
-
Palasdinu: An bayyana Gudanar Da Taron Goyon Bayan Palasdinu A Tehran Da Cewa; Dama ce ta Nuna Raunin 'Yan Sahayoniya A Gabas Ta Tsakiya.
Feb 22, 2017 02:43Mataimakin Shugaban Kungiyar alwifaq ta Bahrain, ya ce; Taron Wata Dama ce ta Nuna Raunin 'Yan Sahayoniya A Gabas Ta Tsakiya.
-
Jِagora: Dukkan Kasashen Musulmi Dole Ne Su Tallafawa Gwagwarmayar Palasdinawa Kan Isra'ila
Feb 21, 2017 12:37Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyeed Aliyul Khamenei ya bayyana cewa dole ne musulmi a ko ina suke a duniya sannan ko mene ne matsayinsu su tallafawa al-ummar Palasdinu kan gwagwarmayan da suke yi da HKI.
-
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadan Turkiya Da Ke Tehran
Feb 20, 2017 14:00Ma'aiktar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadan kasar Turkiya da ke Tehran, domin nuna masa rashin amincewa da kalaman da suka fito daga bakunan Erdogan da kuma ministan harkokin wajen Turkiya na batunci a kan Iran.
-
A Gobe Za A Bude Taron Kasa Da Kasa Kan Taimakon Intifadar Palastinawa A Tehran
Feb 20, 2017 13:57A gobe Talata za a bude babban taron kasa da kasa kan taimaka ma intifadar Palastinawa karo na shida a birnin Tehran, fadar mulkin kasar Iran, wanda gwamnatin kasar ta Iran ke daukar nauyin gudanar da shi a kowace shekara.
-
Larijani: Iran Za Ta Dawo Da Shirin Nukiliyanta Matukar Aka Yi Watsi Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma
Feb 20, 2017 02:52Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da aiwatar da shirin nukiliyanta daga inda ta tsaya kafin cimma yarjejeniyar nukiliya tsakaninta da kasashen 5+1 matukar dai Amurka ta yi watsi da yarjejeniyar.