-
Iran Ta Yi Watsi Da Sabon Takunkumin Amurka, Tana Mai Cewa Za Ta Mayar Da Martani
Feb 04, 2017 02:04Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da sabon takunkumin da Amurka ta sanya mata saboda shirin makamai masu linzaminta na kariya tana mai cewa za ta mayar wa kura da aniyarta.
-
Cin Zarafin Wani Yaro Ba'iraniye A Amurka Ya Dauki Hankula Kafofin Sadarwa
Feb 03, 2017 09:22Cinzarafin wani karamin yaro dan shekaru biyar da haihuwa a filin jirgi na Dalas a jahar Virginia saboda asalin iyayensa Iraniyawa ne, hakan ya dauki hankulan kafofin yada labarai na kasar ta Amurka matuka.
-
Shamkany: Iran Za ta Kalubalanci Tsoma Bakin Kasashen Waje Akan Harkokin Tsaronta
Feb 02, 2017 02:57Babban sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran Ya ce: Duk wani tsoma baki da wata kasar waje za ta yi akan gwajin makamai masu linzami na Iran, to a ta fuskanci maida martani
-
Iran Ta Ce: Dokar Shugaban Amurka Bata Hana Masu Goyon Bayan Ayyukan Ta'addanci Shiga Amurka Ba
Feb 01, 2017 14:25Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Kasashen da suka yi kaurin suna a fagen goyon bayan ayyukan ta'addanci ba su daga cikin jerin kasashen da shugaban kasar Amurka ya hana ba su takardar izinin shiga cikin Amurka.
-
Jagora Ya Ziyarci Hubbaren Imam Khomenei (RA) Farkon Ranakun Fajr
Feb 01, 2017 08:42Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci hubbaren marigayi Imam Khomeni (RA) da wasu daga cikin shahidan juyin Islama, a daidai lokacin da ake fara bukukuwan zagayowar ranakun fajr na juyin Islama a kasar.
-
Iran Ta Ja Kunnen Amurka Dangane Da Kokarin Siyasantar Da Shirin Tsaron Kasarta
Jan 31, 2017 14:25Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya ja kunnen Amurka da ta guji siyasantar da shirin kasarsa na samar da makaman kare kanta yana mai cewa Iran ba ta bukatar izinin wani wajen kare kanta.
-
An Fara Gudanar Da Bukukuwan Ranakun Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci A Iran
Jan 31, 2017 14:23Da safiyar yau ne aka fara bukukuwan ranaku goma na Alfijirin Nasarar juyin juya halin Musulunci a duk fadin kasar Iran don tunawa da shekaru 38 da nasarar da juyin juya halin Musulunci ya samu a kasar ta Iran da kawo karshen mulkin kama karya na 'ya'yan gidan sarautar Pahlawi.
-
Iran Da Faransa Sun Jaddada Bunkasa Alaka A Dukkanin Bangarori A Tsakaninsu
Jan 31, 2017 09:08A ci gaba da gudanar da ziyarar aiki da wata tawagar kasar Faransa karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Jean-Marc Ayrault ke gudanarwa a Iran, bangarorin biyu sun jaddada wajabcin bunkasa alaka a tsakaninsu a dukkanin bangarori.
-
Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addanci A Masallacin Quebec
Jan 30, 2017 14:33Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da wasu 'yan bindiga suka kai a cibiyar Islama ta birnin Quebec na kasar Canada.
-
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Jinjinawa Jami'an Kwana-Kwana Na Kasar Iran
Jan 30, 2017 02:51Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya jinjinawa jami'an kwana-kwana na kasar Iran kan irin sadaukarwar da suka nuna wajen tseratar da rayukan jama'a a gobarar da ta kama a cibiyar kasuwanci ta Plasco da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran.