Pars Today
Na'ibin limamin masallacin jumma'a a nan Tehran, ya yi kira ga kasar Pakistan da kada ta zama sansanon horar da yan ta'adda masu cutar da kasashe makobta.
Shugaban hukumar sadarwan da kimiya da fasaha na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Iran ce ta daya a fagen ci gaban ilmi a cikin kasashen Musulmi sannan ita ce ta 16 a dukkan kasashen duniya.
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Itan (IRGC), ta sanar da cewa wani dan asalin kasar Pakistan ne ya kai harin ta'addancin da ya yi sanadin shahadar mambobinta 27 a makon da ya gabata a yankin Sistan Balouchistan a kudu maso gabashin kasar.
Kakakin ma'aiktar harkokin wajen kasar Iran ya bukaci kasashen Turai su sauke nauyin da ya hau kansu dangane da yerjejeniyar shirin Nkliyar kasar Iran .
Shugaban kasar Iran Dr Hassan ruhani ya yaye labulen fara amfani da wani sabon jirgin ruwan yaki na karkashin ruwa wato Submerrin mai suna Fateh a yau Lahadi a birnin Bandar Abbas na kudancin kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya yi tir da allawadai da kalamman da ya danganta dana kiyaya da marar tushe da mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence ya firta kan kasar ta Iran.
Ministan harkokin wajen Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya gana da babbar jami'ar kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar Federica Mogherini a yau a birnin Munich na kasar Jamus, a gefen taron kasa da kasa kan harkokin tsaro na duniya.
Limamin nda ya jagoranci sallar jumma'a a nan birnin Tehran Hujjatullam Muhammad Jawad Hajj Ali-Akbar ya tattakin ranar 22 ga watan Bahaman naushi ne babba a bakin makiya JMI.
Shugaban kasar Iran Hujjatul Islam Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa manufar taron Sochi na kasar Rasha ita ce yaki da yan ta'adda da kuma dawo da zaman lafiaya a kasar Siriya.
Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khaminae, ya gabatar da ta'aziyarsan ga iyalan shahidan dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar wadanda suka yi shahada a lardin sisatan Buluscistan a jiya da dare.