-
An Gudanar Da Jerin Gwano A Garuruwan Iran Don Yin Allah Wadai Da Masu Haifar Da Fitina A Kasar
Jan 02, 2018 13:42An gudanar da zanga-zangogi a garuruwa masu yawa na kasar Iran a yau din nan Talata don yin Allah wadai da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin gidan kasar da kuma rikice-rikicen da wasu suka haifar a wasu garuruwa na kasar bugu da kari kan nuna goyon bayan ga tsarin Musulunci da ke iko a kasar ta Iran.
-
Jagora: Makiya Suna Amfani Da Kudi Da Makamai Da 'Yan Korensu Wajen Haifar Da Rikici A Iran
Jan 02, 2018 13:40Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar makiya al'ummar Iran suna amfani da hanyoyi mabambanta wajen cutar da al'umma da kuma tsarin Musulunci ta kasar.
-
Iran: Hukumar Leken Asiri Ta Sanar Da Kame Masu Tayar Da Hatsaniya
Jan 01, 2018 15:23A yau litinin ne hukumar leken asirin ta Iran ta ce ma'aikatanta da kuma yan kasa sun gano da kame wadanda suke da hannu a tayar da hatsaniya akan titunan wasu biranen kasar.
-
Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Amurka Bata Da Hakkin Nuna Damuwarta Kan Matsalolin Al'ummar Iran
Jan 01, 2018 03:19Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: A watannin baya-bayan nan shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana al'ummar Iran a matsayin 'yan ta'adda, don haka a halin yanzu baya da hakkin da zai ce yana nuna damuwa kan matsalolinsu.
-
Gwamnatin Iran Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tashin Farashin Kayayyaki
Dec 31, 2017 02:23Gwamnatin kasar Iran ta tabbatar wa al'ummar kasar cewa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen magance matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a kasar lamarin da ya haifar da wasu 'yan zanga-zanga a wasu garuruwa na kasar cikin 'yan kwanakin nan inda mutane suke nuna rashin amincewarsu da wannan yanayin.
-
Iran: Miliyoyin Mutane Ne Suka Fito Don Jaddada Goyon Bayansu Ga Tsarin Musulunci
Dec 30, 2017 15:34Miliyoyin Iraniyawa a duk fadin kasar sun fito kan tituna don tunawa da ranar 30 ga watan Disamban shekara ta 2009, a lokacin da suka dakile shirin manyan kasashen duniya na kawo tashin hankali a kasar don kuma kawo karshen tsarin musulunci a kasar .
-
Majalisar Fayyace Maslahar Musulunci Ta Iran: Ranar 9 Ga Day, Ci Gaban Kumajin Juyi Ne.
Dec 30, 2017 15:32Majalisar ta ce; kumajin da mutane suka nuna a ranar 9 ga watan Day (na hijira shamshiyya) ya kasance a matsayin wani ci gaba mai tarihi na juyin musulunci da mutanen kasar suka nuna basira.
-
Iran Ta Maida Martani Ga Jawaban Jami'an Amurka Kan Wasu Tarurrukan Gangami A Iran
Dec 30, 2017 14:35Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahran Qasim ya bayyana goyon bayan da gwamnatin Amurka ta bayyana ga wasu tarurrukan gangami da aka gudanar a wasu garuruwa a Iran a matsayin yaudara da kuma neman tada fitina a kasar.
-
Jagora:Amurka Ita Ce Kasar Da Ta Fi Barna Da Zalinci A Duniya
Dec 27, 2017 14:43A yayin gananarwa da jami'an gwamnati gami da manbobin kwamitin wa'azi na kasar Iran a wannan Laraba, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ita ce ta fi ko wace gwamnati barna da zalinci a Duniya
-
Majalisar Kasar Iran Ta Kada Kuri'ar Amincewa Da Kudus A Matsayin Helkwatar Kasar Palastinu
Dec 25, 2017 13:40Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ta kada kuri'ar amincewa da kudurin da aka gabatar mata na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Palastinu a matsayin mayar da martani ga kudurin Amurka na sanar da birnin a matsayin babban birnin H.K. Isra'ila.