-
Shugaban Siriya Ya Gode Wa Jagora Da Al'ummar Iran Saboda Goyon Bayansu
Sep 15, 2017 01:19Shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ya bayyana godiyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sauran al'ummar Iran saboda irin goyon bayan da suke ba wa gwamnatinsa a fadar da take yi da ta'addanci.
-
Iran Ta Mayar Da Martani Kan Jawabin Bayan Taron Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa
Sep 14, 2017 00:59Kakakin ma'akatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani ga jawabin bayan taro na ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karo na 146 a birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Laraba.
-
Sharhi: Jagora Yayi Kakkausar Suka Kan Halin Ko In Kula Da Ake Nunawa Musulman Myammar
Sep 13, 2017 01:37Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka dangane da shiru da kuma halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa da masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suke yi dangane da kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar Myammar inda ya ce hanyar magance wannan matsalar ita ce kasashen musulmi su dau matakan da suka dace a aikace da kuma yin matsin lamba ta siyasa da tattalin arziki ga gwamnatin kasar Myammar.
-
Jagora: Magance Matsalar Musulmin Kasar Myanmar Nauyi Ne A Kan Kasashen Musulmi
Sep 13, 2017 01:22Jagoran juyin juya halin musulionci na kasar Iran ya soki kungiyoyin kasa da kasa da masu da'awar kare hakin bil-adama kan yadda suka yi shuru da kuma rashin daukan mataki game da yadda ake yiwa al'ummar musulmi kisan kiyashi a kasar Myammar.
-
Iran Zata Yi Iya Kokarinta Don Ganin An Tsaida Zubar Da Jinin Musulman Myanmar
Sep 12, 2017 14:25Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar zata bi dukkan hanyoyin da suka kamata don ganin ta kawo karshen zubar da jinin musulman kasar Myanmar.
-
Shugaba Ruhani: Kasashen G/Tsakiya Ne Kawai Za Su Iya Tabbatar Da Tsaron Yankin
Sep 11, 2017 13:21Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yayi kakkausar suka ga irin tsoma bakin da manyan kasashen duniya suke yi cikin harkokin cikin gidan kasashen yankin Gabas ta tsakiya yana mai cewa kasashen yankin ne kawai za su iya tabbatar da tsaronsa.
-
Iran: Daliban Jami'o'i Sun Yin Zanga-zangar Tir Da Kisan Musulmin Rohingya
Sep 11, 2017 02:53Daliban sun yi cincirindo a bakin ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Tehran suna masu tir da shirun da duniya ta yi akan kisan na musulmin Rohingya.
-
Shuwagabannin Kasashen Musulmi Zasu Tattauna Batun Kisan Kiyashi A Kan Musulman Myanmar
Sep 10, 2017 10:17Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammaf Jawad Zareef ya bayyana cewa shuwagabvannin kasashen Musulmi Zasu tattauna batun kisan kiyashin da ake wa musulmin kasar Myanmar a taron kan ci gaban ilmi da fasahan da suke gudanarwa a halin yanzu a kasar Qazakistan.
-
Ayat. Kermani: Yayi Allah Wadai Da Kisan Gillan Da Ake Yi Wa Musulmin Myammar
Sep 08, 2017 14:44Limamin da ya jagoranci sallar Jumma'a a nan Tehran, Ayatullah Muwahhedi Kermani a cikin khubobinsa na Jumma'a ya bayyana cewa kasashen duniya basa zatun musulmi suna iya tashi don taimakawa yan'uwansu a kasar Myanmar wadanda sojojin kasar da kuma mabiya addinin Buza suke azbtarwa.
-
Iran: Wajibi Ne Duniya Ta Kawo Karshen Kisan Kiyashin Da Ake Yi Wa Musulmin Rohingya.
Sep 07, 2017 13:30Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Babu wani dalili da zai sa duniya ta zura ido ana yi wa musulmin Rohingya kisan kiyashi.