-
Zaben Amurka: Jam'iyyar Republican Ta Sha Kaye A Zaben Majalisar Amurka
Nov 07, 2018 11:15Jam'iyyar Democrats ta Amurka ta yi nasara a zaben rabin wa'adin zango bayan da ta doke jam'iyyar Republican a majalisar wakilan kasar, lamarin da ake ganinsa a matsayin gagarumin koma baya ga shugaban kasar Donald Trump.
-
Gwamnatin Kasar Amurka Ta Sanar Da Shirinta Na Sake Kakaba Takunkumi Kan Kasar Rasha
Nov 07, 2018 06:21Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar da cewa: Gwamnatin Amurka zata sake kakaba takunkumi kan kasar Rasha.
-
Hatsarin Mota Ya Lashe Rayukan Mutane Tare Da Jikkata Wani Adadi Mai Yawa A Kasar Peru
Nov 07, 2018 06:19Wata motar tirela ta yi taho-mu gama da wata motar bus a kudancin kasar Peru lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane 18 tare da jikkatan wasu 39 na daban.
-
Kasashen Spain Da Rasha Sun Yi Watsi Da Sharuddan Amurka
Nov 06, 2018 17:58Ministocin harkokin wajen kasashen Spain da Rasha sun soki siyasar Amurka musamman kan takunkuman data sake kakaba wa Iran, tare da yin allawadai da sharudan da Amurka ta gindaya kan kasashen dake ci gaba da yin hulda da Iran din.
-
Amurka Ta Gargadi Rasha, China Da Iran Kada Su Yi Katsalanda A Cikin Zaben Kasar
Nov 06, 2018 11:47Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasashen waje, musamman Rasha, China da kuma Iran, kan katsalandi a cikin zaben tsakiyar zango wanda za'a gudanar a yau Talata.
-
Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Nuna Adawarsu Da Sake Kakabawa Iran Takunkumi Da Amurka Ta Yi
Nov 06, 2018 05:25Kasashe da cibiyoyin kasa da kasa na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da sake kakabawa Iran takunkumi da Amurka ta yi, suna masu shan alwashin ci gaba da harkokin kasuwanci da Iran din da kuma riko da yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da kasar.
-
An Caccaki Saudiyya Kan Take Hakkokin Bil'adama A Majalisar Kare Hakkokin Bil'adama Ta MDD
Nov 06, 2018 05:25An caccaki kasar Saudiyya dangane da tarihinta na take hakkokin bil'adama a Majalisar Kare Hakkokin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da kasar take fuskantar tofin Allah daga dukkanin bangarori na duniya kan kisan gillan da ta yi wa dan jaridar kasar Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancinta dake Istanbul na kasar Turkiyya.
-
Kwamitin Tsaro Na Shirin Dage Takunkumin Da Ya Sanya Wa Kasar Eritrea
Nov 06, 2018 05:24Kwamitin tsaron MDD yana shirin dage wa kasar Eritrea takunkumin da ya kakaba mata sakamakon sulhun da suka cimma da kasar Ethiopia duk kuwa da cewa wasu membobin kwamitin suna ganin a ci gaba da matsa wa kasar lamba wajen ganin an kawo karshen rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.
-
'Yan Indonesia 103 Ne Aka Yanke Musu Hukuncin Kisa A Saudiyya A Kasa Da Shekaru Bakwai
Nov 06, 2018 05:16Ma'aikatar harkokin wajen kasar Indonesia ta fitar da rahoton cewa: A tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2018 da ake ciki, 'yan kasarta 103 ne aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya.
-
CIA: Iran Ta Yi Kutse A Cikin Hanyoyin Leken Asiri Na Amurka Ta Hanyar Yanar Gizo
Nov 05, 2018 06:21Wasu tsoffin jami'an hukumar leken asirin kasar Amurka ta CIA sun ce, Iran ta kutsa a cikin tsarin tuntuba da hukumar ta CIA take yin amfani da shi ta hanyar yanar gizo a tsakanin shekarun 2009 zuwa 2013.