Pars Today
Masu kutse a cikin shafuffukan yanar gizo wadanda suke kiran kansu "Black X Team" a kasar Morocco sun kutsa, kuma sun kwace iko da shafin yanar gizo na ofishin shugaban kasar Afrika ta kudu.
Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka kashe mutane biyu.
A yayin da duniya ke ci gaba da tir da kisan da sojojin yahudawan sahayoniya suka wa Palasdinwa 55 a zirin Gaza, kasashen Afrika ta Kudu da kuma Turkiyya sun janye jakadunsu a Israila.
Wasu mahara dauke wukake sun farma wa wani masallacin 'yan shi'a a yankin KwaZulu-Natal dake Afrika ta Kudu, inda suka kashe limanim masallacin tare da raunana mutum biyu.
Gamayyar kungiyoyin kwadago a kasar Afirka ta kudu na gudanar da gangami da jerin gwano a biranan kasar, domin nuna rashin amincewa da tsarin albashi mafi karanci.
Jami'an 'yan sanda a kasar Afirka ta kudu sun sanar kashe wani matashi a zanga-zangar da ake yi a wasu yankunan kasar, domin nuna rashin amincewa da barna da dukiyar kasa.
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kafa komitin masanan tattalin arziki da yan kasuwa don samarwa kasar jari na akalla dalar Amurka billyon 100 daga ciki da wajen kasar.
Kotun birnin Durban, a Afrika Ta Kudu, ta dage zaman shari'ar da ake wa tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma, har zuwa ranar 8 ga watan Yuli mai zuwa.
A yau Juma'a, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gurfana a gaban babbar kotun birnin Durban saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa kan wani ciniki na makamai da suka kai dala biliyan 2.5 da aka yi tun a shekarun 1990.
Babban sakatare na MDD, Antonio Guterres ya nuna alhini kan mutuwar Winnie Madikizela-Mandela, tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela kuma shugaban gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata.