Pars Today
Wasu sanannun 'yan siyasa 14 na kasar Aljeriya sun aike da wasika zuwa ga shugaba Abdelaziz Bouteflika, inda suka bukaci kadda ya sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za gudanar a shekarar 2019 mai zuwa.
Shugaban jam'iyyar Social Democratic Party a kasar Aljeriya ya bayyana cewa: Bakar siyasar Amurka tana barazana ga zaman lafiyan duniya musamman yankin gabas ta tsakiya.
Ministan harakokin wajen Masar ya yaba da tattaunawar da makwabtar Libiya suke yi a Aljeriya domin lalubo hanyar magance rikicin kasar Libiya
An Kai harin ta'addanci a jahar Sidi Bel Abbès dake arewa maso yammacin kasar Aljeriya, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutun biyu.
Gwamnatin kasar Algeria zata sake nazarin dangantakar diblomasiyyar kasar da kasar Morooc bayan tuhumarta da hada kai tare da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.
Akalla mutane 15 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon nutsewar wani kwale-kwale da yake dauke da wasu 'yan ci rani da ke shirin tsallakawa zuwa nahiyar turai ta barauniyar hanya daga gabar ruwan kasar Aljeriya.
Shugaban Majalisar Koli ta musulinci a kasar Aljeriya ya bayyana cewa wanzuwar akidar salafiyanci ita ce ta bata tunanin al'umma a kasar da kasashen musulmi.
Jam'iyyar FLN mai mulki a Aljeriya, ta bukaci shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika, da ya yi tazarce ta hanyar neman wani wa'adin mulki karo na biyar, duk da rashin lafiyar da yake fama da shi.
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da kame wasu 'yan ta'addan takfiriyya hudu da suka hada da wani gawuraccen kwamanda daga cikinsu.
Duniya na ci gama da aike wa da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Aljeriya da al'ummarta, biyo bayan mumunnan hatsarin jirgin saman soji da ya yi ajalin mutum 257