Masar Ta Yaba Da Tattaunawar Aljeriya Kan Rikicin Libiya
Ministan harakokin wajen Masar ya yaba da tattaunawar da makwabtar Libiya suke yi a Aljeriya domin lalubo hanyar magance rikicin kasar Libiya
A wata tattaunawa da yayi tare da jaridar kasar Aljeriya, Samuh Shukry ministan harakokin kasar Aljeriya ya kara da cewa kasashen Masar da Tunusiya nada ra'ayi iri guda na magance rikicin kasar Libiya, kuma tattaunawar da kasashen ukun suka yi kwanaki biyu da suka gabata a Aljeriya nada amfani sosai.
Shukry ya ce tattaunawar da aka yi cikin sirri, ko wani bangare ya bayyana ra'ayinsa kan yadda za a magance rikicin kasar ta Libiya, sannan kuma an yi musayar ra'ayi kan yadda za a yi aiki tare wajen magance rikicin siyasa da na kabilanci a kasar.
Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici ne, tun da bayan da dakarun Amurka da na kungiyar Nato suka kifar da gwamnatin marigayyi Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011.