Ci Gaba Da Zanga-Zanga A Kasar Aljeriya
(last modified Tue, 19 Mar 2019 06:37:55 GMT )
Mar 19, 2019 06:37 UTC
  • Ci Gaba Da Zanga-Zanga A Kasar Aljeriya

Bayan kwashe wasu makoni, da al'ummar kasar Aljeriya suke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsayawa takarar Abdelaziz Bouteflika a zaben shugaban kasar karo na biyar, daga karshe shugaba Bouteflika ya janye takarar tasa tare da daga zaben shugaban kasar har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba

A ranar 18 ga watan Afrilu mai kamawa ne ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasar a Aljeriya, saidai cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Aljeriya ta fitar ta ce an dage zaben shugaban kasar ne domin gudanar da sauye-sauye musaman ma a bangaren siyasa, da tattalin arziki, sannan za a gudanar da zaben raba gardama kan kwaskwarimar da za a yi wa kundin tsarin milkin kasar, idan ya samu amincewa, sai a gudanar da zaben shugaban kasar.

Wannan mataki da gwamnatin Aljeriyar ta dauki ya fuskanci adawa daga jam'iyyun adawar kasar.

idan ba a manta ba tun a watan Favrayun da ya gabata ne kungiyoyin farar hula da na 'yan siyasa na kasar Aljeriyan suka fara gudanar zanga-zangar nuna adawa da tsayawar takarar shugabancin kasar a karo na biyar, kasancewar yawan shekaru da kuma rashin lafiya da yake fama da ita, lamarin da wasu ke ganin cewa ba shike gudanar da ayyukan milki a kasar ba.

A halin da ake ciki, mafi mahimanci ga al'ummar kasar Aljeriyan, a samu shugaban kasar da zai fitar da wasu sabin shirye-shiryen da zai magance matsalolin matasa da farfado da tattalin arzikin kasar, a bangaren siyasa kuma, akwai bukatar samar da 'yancin fadar albarkacin baki ga 'yan siyasa da 'yan jaridu, wanda hakan zai sanya tsarin Dimokaradiyar kasar ya bunkasa.

Duk da cewa  da dama daga cikin kungiyoyin siyasa da na 'yan adawa sun yi murna da janyewar takarar shugaba Boutelfika a zaben shugaban kasar, to saidai dage zaben da ya yi, ya rusa duk wani fata na siyasar kasar ta Aljeriya.

Da dama daga cikin 'yan siyasa da al'ummar kasar Aljeriya na ganin cewa dage zaben shugaban kasar da kuma rashin sanar da wata rana na gudanar da zabe, ya sanya damuwa a zukatan 'yan siyasar kasar sannan sun ce wannan batu ya sabawa tsarin Demokaradiya.

Yayin da yake ishara kan manufar Shugaba Abdul-azizBoutelfika na dage zaben shugaban kasar, mai magana da yawun jam'iyar Tala'i'i Alhurriyat(طلائع الحریات) Ahmad Azimi ya ce manufar shugaba Boutelfika shi ne ci gaba da zama a kan karagar milki, kuma hakan ya sabawa doka, bayan ga hakan Azimi ya ce irin wannan alkawari irinsa ne shugaba Boutelfika ya yi a shekarar 2011, amma bai cika ba.

Amma kuma a bangare guda, kungiyoyin kasa da kasa gami da wasu shugabanin kasashen Duniya sun ya bawa shugaba Boutelfika kan matakin da ya dauka na jenyewa daga takarar shugabancin kasar a karo na biyar, wanda suka ce hakan zai hana kasar shiga cikin rikicin siyasa.

Kungiyar tarayya Afirka (AU) ta yi kira ga bangarori a Aljeriya dasu tattaunada juna domin cimma daidaito akan matakin da shugaban kasar ya dauka na janye wa daga takara shugaban kasa a karo na biyar.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin kungiyar Musa Faki Mahamat ya sanya wa hannu, kungiyar ta AU, ta jinjinawa shugaba Butaflika akan matakin da ya dauka.

To saidai a halin da ake cikin Duniya ta zura, kan ranar da gwamnatin Aljeriya za ta sanya a gudanar da zabe a kasar da kuma yadda za a gudanar da shi.