Mar 19, 2019 09:46 UTC
  • Sojojin Aljeriya Sun Dauki Alkawarin Magance Matsalar Kasar

A yayin da Al'ummar kasar Aljeriya ke ci gaba da nuna adawa da gwamnati, shugaban Dakarun hadin gwiwa na kasar ya tabbatawa al'umma cewa dakarun tsaron kasar zu su kasance a tare da al'ummar kasar

Kamfanin dillancin labaran Reuteus daga birnin Alje ya nakalto Janar Ahmad Qa'id Saleh shugaban rundunar tsaron hadin gwiwar kasar, yayin da yake ishara kan tabbacin da ya baiwa al'ummar kasar na magance matsaloli da rikicin siyasar da kasar take ciki a yau, ya ce tabbas Sojojin Aljeriya za su kasashe a bayan al'ummar kasar.

Janar Saleh ya ce Rundunar tsaron kasar nada tabbacin cewa al'ummar kasar ba za ta amince da katsa landan din duk wata kasar waje ba wajen tayar da hargitsa gami da rashin tsaro a kasar ba.

Duk da cewa Shugaba Abdu-Aziz Bouteftika ya janye daga takarar shugabancin kasar da za a yi nan gaba, da kuma sanar da dage ranar zaben, yankuna da dama na Aljerian ya ci gaba da fuskantar zanga-zangar neman shugaba Bouteflika ya yi muranus daga kan mikaminsa

Tags