Morocco : Ba Zamu Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Aljeriya Ba
Kasar Morocco, ta sanar da cewa ita fa ba zata tsoma baki ba a cikin al'amuran cikin gidan makobciyar Aljeriya ba, dangane da zanga zangar dake faruwa ta kin jinin sake tsayawa takarar shugaban Abdelaziz Bouteflika.
Da yake sanar da hakan, ministan harkokin wajen kasar ta Morocco, a wata sanarwar da aike wa kamfanin dinlancin labaren AFP, Nasser Bourita, ya ce Morocco ta dau matakin nisanta kanta daga yin duk wani tsokaci ko tsoma baki a halin da ake ciki a Aljeriya.
Morocco da Aljeriya dake makobtaka sun jima basa jituwa da juna musamman kan batun batun yankin sahara na yamma, wanda Aljeriya ke goyan bayan 'yan Polisario dake fafatukar neman samun 'yancin kai.
Tun a shekara 1994 ne iyaka ta tsakanin manyan kasashen biyu na yankin Magreb ke rufe.