Pars Today
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayya Afrika, sun bukaci ganin an warware rikicin kasar Libiya, ta hanyar siyasa.
Kasar Chadi ta sanar da rufe kan iyakarta da kasar Libiya, har sai abunda hali ya yi, kamar yadda ministan cikin gida na kasar, Mahamat Abba Ali Salah ya sanar.
Tawagar wakilai na musaman na Majalisar Dinkin Duniya sun bada sanarwan cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnatin hakin kan kasa da babban hafsan sojin kasar kan yadda za a gudanar da zabe a Libiya
Sojojin kasar Libya karkashin shugabancin Janar Halifa Haftar mai ritaya sun sami nasarar korar yan ta'adda daga garin Murzuk babban birnin lardin Murzuk dake kudu maso yammacin kasar.
Majalisar dinkin duniya ta jadadda bukatar ganin an kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Libiya.
Kungiyar tarayya Afrika (AU), ta yi kira ga manyan kasashen duniya dasu daina tsaoma baki a cikin al'amuran cikin gida na kasar Libiya da rikici ya daidaita.
Kamfanin dillancin labarun Anatoli ya nakalto cewa; Bayan kwanaki da sojojin na Halifa Haftar su ka killace yankin na al'Shararah, wanda shi ne wuri mafi girma na man fetur a kasar ta Libya, a karshen sun kwace iko da shi a jiya Litinin
Gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya ta bukaci majalisar sulhu ta majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin dakatar da dakarun tsaron kasar karkashin janar Khalifa Haftar ci gaba da hare-haren da suke kaiwa kudancin kasar
Majiyar sojojin kasar Libya wadanda suke biyayya ga Janar Halifa Haftar mai ritaya ta bara labarin cewa sojojin kasar sun sami nasara mamaye garin Drne dake gabacin kasar gaba dayansa.
Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa fada ta sake barkewa a garin Sabha na kudancin kasar