Feb 28, 2019 18:32 UTC
  • An Cimma Matsaya Kan Gudanar Da Zabe A Libiya

Tawagar wakilai na musaman na Majalisar Dinkin Duniya sun bada sanarwan cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnatin hakin kan kasa da babban hafsan sojin kasar kan yadda za a gudanar da zabe a Libiya

 Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto tawagar wakilan majalisar dinkin duniya na musaman kan al'amuran da suka shafi kasar Libiya na cewa an cimma matsaya tsakanin Khalifa Haftar babban hafsan sojin kasar da Fayez al-Sarraj shugaban majalisar zartarwa ta kasar Libiya kan yadda za a gudanar da zabe a kasar

An cimma wannan matsaya ne a ranar Larabar da ta gabata a Abu Dabi babban birnin hadaddiyar daular larabawa, a wani zama da aka gudanar tsakanin bangororin biyu bisa sa ido na tawagar wakilan MDD na musaman kan kasar ta Libiya, banda haka, an tattauna a zaman kan yadda za a samar da tsaro a kasar.

bayan kamala taron dai, bangarorin biyu sun bayyana wajibcin sasantawa a tsakanin al'ummar kasar ta Libiya.

Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici yaki tun bayan borin da matasan kasar suka yi a shekarar 2011, inda kasar Amurka da Dakarun tsaron Nato suka shiga kasar suka kuma kashe marigayyi kanar Mu'amar Kaddafi, sannan daga shekarar 2014,zuwa yanzu, kasar na da gwamnatoci da Majalisun dokoki guda biyu, akwai ta birnin Tripoli wacce ke samun goyon bayan kasashen Duniya, da kuma ta birnin Tabruk dake samun goyon bayan babban hafsan sojin kasar Halifa Haftar.

Tags