Mar 14, 2019 08:37 UTC
  • MDD Da AU Sun Goyi Bayan Warware Ricikin Libya Ta Hanyar Siyasa

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayya Afrika, sun bukaci ganin an warware rikicin kasar Libiya, ta hanyar siyasa.

Da take sanar da hakan mataimakiyar babban sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa da samar da zaman lafiya, Rosemary DiCarlo da kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka(AU) mai kula da zaman lafiya da tsaro, Ismail Sharqi, sun jaddada goyon bayansu na daidaita ricikin kasar Libya ta hanyar siyasa.

Jami'an biyu sun yi wadannan kalamai ne jiya Laraba, yayin wata ganawa da kwamandan sojojin kasar mai hedkwata a gabashin kasar, janar Khalifa Haftar.

Kasar Libya dai ta tsunduma cikin tashin hankali da rikicin siyasa tun bayan kifar da gwamnatin mirigayi Mu'ammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, wanda ya kai ga samun sabani tsakanin gwamnatocin yammaci da gabashin kasar.

Tags