Pars Today
Babban sakatare na MDD, Antonio Guteres, ya bukaci kasashen duniya dasu kara kaimi wajen samar da tallafi ga dubban mutanen da ifti’la’in mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ya shafa a gabashin Afrika.
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayya Afrika, sun bukaci ganin an warware rikicin kasar Libiya, ta hanyar siyasa.
Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci mahukuntan Faransa dasu gudanar da bincike kan amfani da karfi na jami'an 'yan sanda kan masu zanga zanga a kasar da ake kira da masu ''dorawa riga''.
Shugaba Donald Trump, na Amurka ya nada jami'ar diflomatsiyar kasar, Kelly Knight Craft, a matsayin sabuwar jekadiyar kasar a MDD.
Wakilin kasar Venezuela a MDD ya bukaci jakadodin kasashen Duniya 46 na majalisar da suka gudanar da zama da nufin tabbatar da alkawarin da Majalisar ta dauka na nuna adawa da barazanar kai harin soja a kan kasar
Majalisar dinkin duniya ta jadadda bukatar ganin an kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Libiya.
Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da cimma wata yarjejeniya tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen, wacce ta tanadi janye masu dauke da makamai a birnin Hodeida.
A ci gaba da gangamin neman hakkin komawar Falastinawa 'yan gudun hijira a Gaza, sojojin Isra'ila sun kashe Falastinawa tare da jikkata wasu.
Shugaban kungiyar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika (SADC) kana shugaban kasar Namibia Hage Geingob a ranar Lahadi ya gayyaci babban sakataren MDD Antonio Guterres domin tattauna hanyoyin warware dambarwar siyasa a kasashen Zimbabwe da jamhuriyar demokaradiyar Kongo DRC.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq ya sanar a jiya juma'a ce kwamitin sulhu na Majalisar shi kadai ne ke da hakin fayyace shirin sararin samaniya da makamai masu Linzami na kasar Iran ko ya ci karo da doka mai lamba ta 2231 ba wata kasa ba.