Mar 06, 2019 12:58 UTC
  • Faransa : MDD Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Amfani Da karfi Kan Masu Bore

Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci mahukuntan Faransa dasu gudanar da bincike kan amfani da karfi na jami'an 'yan sanda kan masu zanga zanga a kasar da ake kira da masu ''dorawa riga''.

Da take sanar da hakan gaban majalisar kare hakin bil adama a Geneva, babbar kwamishiniyar hukumar, Michelle Bachelet, ta ce suna goyan bayan gwamnatin Faransa akan ta ci gaba da shirinta na tattaunawa, amma muna kiran da a gudanar da bincike cikin gaggawa kan duk zarge zargen da ake na amfani da karfi kan masu boren.

Tun dai farkon boren na masu dorawar riga a Faransa, wnda ya faro a tsakiyarwatan Nowamba na shekara data gabata, ma'aikatar bincike ta 'yan sanda kasar (IGPN) ta samu korafe korafe kusan dari na zargin 'yan sanda da amfani dakarfi kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa dake da nasaba da manufofin gwamnatin Shugaba Emanuel Macron na karin haraji da ya shafi masu karamin hali.

Dayewa daga cikin masu zanga zanga sun ce sun samu raunuka sakamakon amfani da da harsashai nau'in LBD na garkuwa da 'yan sanda ke amfani dasu, wanda yana daya daga cikin batutuwan da suka tayar da zazzafar muhawara a kasar ta Faransa.

Tags