Yemen : An Cimma Yarjejeniyar Janye Mayaka Daga Hodeida
Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da cimma wata yarjejeniya tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen, wacce ta tanadi janye masu dauke da makamai a birnin Hodeida.
Yarjejeniyar ta tanadi yadda za'a fara aiwatar da shirin janye mayakan a matakin farko daga birnin na Hodeida wanda ya kunshi tashar jiragen ruwa a yammacin kasar da yaki da daidaita, saidai ba tare da bayyana takamaimai ranar da za'a fara aiwatar da shirin ba.
Shirin farko ya tanadi janyewar mayaka daga tashar ruwa ta Hodeida, da Saleef, da kuma ta Ras Issa a birnin wanda ta nan ne ake shigar galibin kayan agaji.
MDD, dai na fatan, wannan shirin, zai bada damar shigar da tallafin abinci dana magunguna a wanann kasa ta Yemen, da yaki ya jefa 'yan kasar miliyan 14 cikin bala'in yunwa.
Shirin janye mayakan daga yankin na Hodeida, ya fuskanci tsaiko kasancewar yana kunshe ne a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka cimma a ranar 18 ga watan Disamban bara a Sweden, wacce kuma ta tanadi a fara aiwatar da shirin makwanni biyu bayan yarjejeniyar ta Sweden.
Nan kuma da mako guda ne ake sa ran bangarorin zasu hadu a zagaye na biyu domin daddale mataki na biyu na janye mayaka daga yankin da kuma musayar fursunoni.