Feb 11, 2019 05:42 UTC
  • SADC Da MDD Sun Tattauna Hanyoyin Warware Rikicin Zimbabwe Da Congo

Shugaban kungiyar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika (SADC) kana shugaban kasar Namibia Hage Geingob a ranar Lahadi ya gayyaci babban sakataren MDD Antonio Guterres domin tattauna hanyoyin warware dambarwar siyasa a kasashen Zimbabwe da jamhuriyar demokaradiyar Kongo DRC.

A wata sanarwar da aka fitar daga ofishin shugaban kasar Namibian, M. Geingob ya ce, ya gayyaci babban jami'in MDD ne a gefen taron kungiyar tarayyar Afrika AU a Habasha domin yi masa karin haske game da halin da ake ciki a kasashen Zimbabwe da DRC.

Mista Geingob, ya ce sun tattauna game da yanayin siyasar da ake ciki a DRC, Zimbabwe da yankin kudancin Afrika baki daya. inda mika cimma matsaya game da aikin hadin gwiwa tsakanin SADC da MDD domin inganta yanayin shugabanci da kyautata rayuwar al'ummar shiyyar SADC," in ji Geingob.

A halin yanzu Zimbabwe tana fuskantar boren al'ummar kasar sakamakon matsanancin tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa dake addabar talakawa masu karamin karfi a kasar, lamarin da ya tunzura jama'a suka fita titunan kasar don yin zanga zangar adawa da kara farashin man fetur da aka yi a kasar a watan jiya.

Haka zalika ana zargin sojojin kasar da aikata laifukan take hakkin bil adama a kasar ko da yake shugaban kasar Zimbabwen Emmerson Mnangagwa yana cigaba da bayyanawa takwarorinsa dake shiyyar cewa komai yana tafiya daidai a kasarsa. 

Tags