Mar 04, 2019 12:06 UTC
  • Chadi Ta Rufe Kan Iyakarta Da Libiya

Kasar Chadi ta sanar da rufe kan iyakarta da kasar Libiya, har sai abunda hali ya yi, kamar yadda ministan cikin gida na kasar, Mahamat Abba Ali Salah ya sanar.

Ministan ya sanar da wannan matakin ne tun daga lardin Kuri-Bugudi, dake yankin arewa maso yammacin kasar ta Chadi, inda ya gudanar da wani ran gadi wata guda bayan da wani ayarin 'yan tawaye da ya shigo kasar daga LIbiya.

Yankin na Kuri-Bugudi, a cewar mahukuntan kasar ta Chadi, ya kasance wata matatara 'yan daba, da 'yan ta'adda da kuma 'yan tawaye, kuma duk wani mahaluki dake a yankin za'a daukansa a matsayin dan ta'adda, inji ministan Abba Ali Salah.

Kuri-Bugudi, yanki ne da ya kunshi zinari dake a yankin tsaunuka dake akan iyakoki biyu na kasashen Chadi da Libiya, wanda kuma yake janyo hankalin 'yan Chadi da kuma 'yan kasashen waje da dama.

A karshen watan Janairu da ya gabata, wasu 'yan tawayen Chadi suka yunkuri shiga kasar ta Chadi daga Libiya, wanda kuma daga bisani Faransa ta kaiwa hari don murkushe anniyarsu.

Tags