Fada Ta Sake Barkewa A Garin Sabha Na Kudancin Kasar Libya
Feb 06, 2019 04:10 UTC
Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa fada ta sake barkewa a garin Sabha na kudancin kasar
Jaridar Al-Yaumul Jadid ya nakalto jami'an tsaron kasar ta libya masu goyon bayan gwamnatin Hadin kan kasa karkashin Firai Minista Fa'iz Suraj suna fadar haka. Hamid Al-attabi komandan rundunar ta 6 ya bayyana cewa sojojinsa sun janye daga birnin Sabha, birni mafi girma a kudu maso yammacin kasar ta Libya don kasuwarsu wajen yakar sojojin Khalifa Haftar.
Labarin a halin yanzu sojojin Halifa Haftar suna shiga birnin don karban iko da shi. Birnin Sabha dai yana da tazarar kilomita 750 daga birnin Tripoli babban birnin kasar ta Libya. kuma yana da mutane sun kai dubu 100.
Tags