Pars Today
Gwamnatin kasar Algeria ta yi watsi da bukatar ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka na shigo da sojojinta cikin kasar don kare ofishin jakadancinta a kasar.
Shugaban cibiyar kare hakin bil-adama na kasar Aljeriya ya soki cinikayyar bakin haure a kasar Libiya.
Ministocin harkokin wajen kasashen Aljeriya, Masar da Tunusiya sun yi gargadi kan hatsarin komawar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish kasashensu da suke nahiyar arewacin Afrika.
Daya daga cikin 'yan gwagwarmayar Aljeriya da suka yi yakin 'yantar da kasar daga mulkin mallakar kasar Faransa, kuma mamba a kungiyar National Liberation Front ta kasar ya bayyana cewa: Mahukuntan Saudiyya sun hada kai ne da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da nufin wanzar da bakar siyasarsu a yankin gabas ta tsakiya.
Ministan harkokin wajen kasar Faransa ya bayyana damuwarsa da komarwar mayakan kungiyar Daesh kasashensu na asali bayan korarsu da aka yi a kasashen Iraqi Siria da Lebanon.
Firayi ministan kasar Aljeriya, Ahmed Ouyahia, ya bayyana cewar wasu kasashen larabawa sun kasashe zunzurutun kudaden da suka kai Dala Biliya 130 da nufin ruguza kasashen Siriya, Libiya da Yemen.
Wakilin kasar Aljeriya a MDD Mohammed BESSEDIK ya bukaci a gudanar da canji tare da bawa kasashen Afirka kujeru biyu na din din din a kwatinin tsaro na MDD.
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ce ta sanar da gano maboyar 'yan ta'addar a garin Boumerdes tare da rusa ta.
A yau juma'a me sojojin kasar ta Aljeriya suka fitar da bayani da a ciki suka bayyana kashe 'yan ta'adda 14 da kuma kame 31 a cikin wara goda.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan gwamnatin Aljeriya dangane da yadda take gudanar da mummunar mu'amala ga bakin haure musamman fitar da su daga cikin kasarta ta hanyar musgunawa.