Nov 02, 2017 06:18 UTC
  • Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty International Ta Yi Suka Kan Kasar Aljeriya

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan gwamnatin Aljeriya dangane da yadda take gudanar da mummunar mu'amala ga bakin haure musamman fitar da su daga cikin kasarta ta hanyar musgunawa.

A bayanin da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta fitar ya yi Allah wadai da yadda mahukuntan Aljeriya suke gudanar da mummunar mu'amala ga bakin haure ba tare da yin la'akari kan irin mummunan halin da bakin haure suke ciki ba musamman a fagen kuncin rayuwa da irin mummunan kangin da suke fuskanta a muhallinsu.

Bayanin na kungiyar Amnesty International ya kuma fayyace cewa: Yawan fataucin bakin haure da 'yan cirani zuwa kasar Aljeriya daga yankunan sahara da suke nahiyar Afrika, yana daga cikin dalilan wurga bakin hauren cikin mawuyacin hali a fagen rayuwa.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta kara da cewa: Daga watan Satumban wannan shekara ta 2017 zuwa yanzu, wato a cikin watanni biyu kacal, bakin haure fiye da 2000 ne jami'an tsaron Aljeriya suka kame a cikin kasar.       

Tags