-
Kungiyar AU Ta Dakatar Da Aika Sojoji Zuwa Kasar Burundi
Jan 31, 2016 13:11Kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta dakatar da shirinta na tura dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar dubu biyar zuwa kasar Burundi don tabbatar da zaman lafiya a kasar sakamakon ci gaba da nuna adawa da hakan da gwamnatin kasar take yi.