Kungiyar AU Ta Dakatar Da Aika Sojoji Zuwa Kasar Burundi
Kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta dakatar da shirinta na tura dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar dubu biyar zuwa kasar Burundi don tabbatar da zaman lafiya a kasar sakamakon ci gaba da nuna adawa da hakan da gwamnatin kasar take yi.
Yayin da yake sanar da wannan matsayar, kwamishinan kungiyar AU din na tabbatar da tsaro da zaman lafiya Smail Chergui, ya shaida wa manema labarai a yau din nan Lahadi a helkwatar kungiyar da ke birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia cewa an dakatar da tura sojoji 5000 din har sai an sami yarda da kuma izinin gwamnatin kasar Burundin.
Mr. Chergui ya kara da cewa yanzu dai kungiyar za ta tura da wata tawaga zuwa kasar Burundin don tattaunawa da gwamnatin kasar kan wannan batu a kokarin da ake yi na shanyo kan shugaba Nkurunziza ya amince da wannan bukata ta Tarayyar Afirkan.
A baya dai shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza ya ce al'ummar kasar Burundin za su dauki duk wani mataki da kungiyar ta AU za ta daukana tura sojoji zuwa kasar a matsayin shelanta yaki a kan kasar.